Rikici Ya Salwanta Rayukan Mutum 16 A Kudancin Somaliya
Wani rikici tsakanin mayakan sa kai da mayakan kungiyar Ashabab ya salwanta rayukan mutum 16 a kudancin Somaliya
Hukumomin kasar Somaliya sun sanar da cewa wani fada ya barke tsakanin dakarun sa kai na Jubaland da mayakan kunmgiyar ta'addancin nan ta Ashabab, lamarin ya yi sanadiyar mutuwar mutum a bangaren mayakan sa kai da kuma mutum 11 a bangaren kungiyar Ashabab.
Jamal Hasan Fari daya daga cikin komondojin mayakan sa kai ya ce baya ga mutunan da suka rasa rayukansu akwai wasu mutum 7 da suka samu rauni a bangaren mayakan sa kai.
Hasan Fari ya ce rikicin ya barke ne a yayin da suka samu labarin cewa mayakan kungiyar Ashabab din na shirin kai musu hari.
Tun a cikin 2012 ne dai kungiyar ta al-shabab wacce reshe ne na kungiyar alqaida, ta kai munanan hare-hare acikin kasar Somaliya da kuma Kenya.