An Kama Sojojin Da Suka Halbe 'Yar Shekara 9 A Somaliya
(last modified Fri, 21 Sep 2018 06:34:59 GMT )
Sep 21, 2018 06:34 UTC
  • An Kama Sojojin Da Suka Halbe 'Yar Shekara 9 A Somaliya

Jami'an 'yan sanda sun sanar da kama wasu sojoji hudu a Somaliya bayan da aka harbe wata 'yar shekara tara a babban birnin kasar Mogadishu.

A ranar talatar da ta gabata ce wasu sojoji suka yi harbi domin samun hanyar ficewa yayin da suka isa wata hanya mai cinkoso, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wata yarinya mai shekaru tara a Duniya

Kungiyar kare hakkin bil adama Amnesty International ta ce yarinyar mai suna Deqa Dahir ta mutu, kuma wata yarinyar ta ji rauni lokacin da harsasai suka bula motar makarantar da ke dauke da su a cunkoson ababen hawa.Kungiyar ta kara da cewa sojojin sun bude wuta a kokarinsu na bude wa motarsu hanya.

An binne yarinyar a jiya Alhamis, kwana biyu bayan da aka kashe ta.Yarinyar dai tana shekararta ta farko ne a makaranta, kuma tana kan hanyarta ta komawa gida ne cike da farin ciki, lokacin da aka harbe ta.

Shugaban Somaliya ya gana da iyalan Dahir, a yayin da jama'a ke nuna fushinsu kan harbin da aka yi.