Tanzania : Sama Da Mutum 200 Suka Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33287-tanzania_sama_da_mutum_200_suka_mutu_a_hatsarin_jirgin_ruwa
Hukumomi a Tanzania, sun sanar da cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin ruwa da ya kife a tafkin Victoria, ya haura sama da 200, a yayin da aka shiga kwanaki uku na aikin ceton da ake.
(last modified 2018-09-22T12:44:07+00:00 )
Sep 22, 2018 12:44 UTC
  • Tanzania : Sama Da Mutum 200 Suka Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa

Hukumomi a Tanzania, sun sanar da cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin ruwa da ya kife a tafkin Victoria, ya haura sama da 200, a yayin da aka shiga kwanaki uku na aikin ceton da ake.

Da yake bayyana hakan ministan sufirin kasar, a gidan radiyon kasar, na TBC, Isack Kamwelwe, ya ce a ranar yau Asabar, adadin mutanen da suka mutu a hatsarin jirgin ruwan ya kai 207. 

Dama kafin hakan jama'ar kasar da dama sun nuna fargaba akan inda adadin zai kai, ganin cewa ana cikin aikin ceton.

Kawo yanzu dai babu tabas akan musababin hatsarin jirgin amma tuni aka fara maida hankali kan lodin mutane fiye da kima da kuma ganganci.

Babban hafsan sojin kasar dai Janar, Venance Mabeyo, ya bayyana wa gidan gidan radiyon kasar cewa a yau ne za'a kawo karshen aikin ceton. 

Tuni dai aka ayyana zaman makoki na kwanaki hudu a kasar.