An Gudanar Da Taron Sulhu Tsakanin Sudan Da Sudan Ta Kudu
(last modified Sun, 23 Sep 2018 06:44:01 GMT )
Sep 23, 2018 06:44 UTC
  • An Gudanar Da Taron Sulhu Tsakanin Sudan Da Sudan Ta Kudu

Kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun tattaunawa kan batun aiki tare na tabbatar da sulhu da kuma karfafa alaka tsakanin kasashen biyu

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar China ya nakalto ministan harakokin wajen kasar Sudan al-Dirdiri Mohamed Ahmed na cewa a ranar juma'ar da ta gabata shugaban kasar Sudan Omar El-Bashir da takwaransa na kasar Sudan ta kudu Salva keir sun tattaunawa a fadar shugaban kasar ta Sudan, inda suka yi alkawarin aiki tare domin tabbatar da sulhu mai dorewa da kuma karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.

A nata bangare ma'aikatar sadarwa ta kasar Sudan ta kudu ta sanar da cewa gwamnatin kasar ta bukaci hukumomin birnin Khartoum da su taimakawa kasar wajen magance matsalolin dake tattare da gudanar da yarjejjeniyar sulhu tsakanin gwamnati da 'yan tawayen kasar.

A watan da ya gabata ne shugaban kasar sudan ta kudu da tsohon mataimakinsa kuma madugun 'yan tawayen kasar Riek Machar suka cimma yarjejjeniyar karshe kan yadda a gudanar da yarjejjeniyar sulhu da suka cimma a birnin Adis Ababa na kasar Habasha.