Najeriya : Buhari Zai Halarci Taron Shekara Shekara Na MDD
A yau lahadi ne ake saran shugaban tarayyar Najeriya Mohammadu Buhari zai je birnin New York na kasar Amurka don halattan taron shekara shekara na majalisar dinkin duniya karo na 73.
Jaridar Vanguad ta Najeriya ta bayya cewa shugaban zai yi jawabi ga babban zauren majalisar dinkin duniya a ranar talata mai zuwa ranar da za'a bude taron.
Banda haka ana saran shugaban zai halarci tarurruka da dama daga ciki harda na girmama tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Nelson Mandela da kuma na yaki da ayyukan ta'addanci. A cikin tawagar shugaban, banda matarsa akwai wasu gwamnanoni da ministoci da kuma wasu manya manyan jami'an gwamnati.
Mai bawa shugaban kasa shawara kan lamuran watsa labarai Chief Femi Adesina ya bayyana cewa Matar shugaban zata halatci taron matan shuwagabannin kasashen duniya da kuma wasu tarurrukan da suka shafi mata.
Sannan a gefen taron kuma ana saran shugaban zai gana da shuwagabannin kasashen duniya da dama da kuma wasu yan Najeriya masu zama a kasar Amurka.