An Sace Ma'aikatan Wani Jirgin Ruwan Kasuwanci Yan Kasar Swizland A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33301-an_sace_ma'aikatan_wani_jirgin_ruwan_kasuwanci_yan_kasar_swizland_a_najeriya
Ma'aikatan wani jirgin ruwan kasuwanci 12 ne aka sace a kudancin tarayyar Najeriya.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Sep 23, 2018 11:49 UTC
  • An Sace Ma'aikatan Wani Jirgin Ruwan Kasuwanci Yan Kasar Swizland A Najeriya

Ma'aikatan wani jirgin ruwan kasuwanci 12 ne aka sace a kudancin tarayyar Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto majiyar kamfanin jiragen ruwa mai suna Massoel Shipping na kasar Swizland yana fadar haka a ranar Asabar da ta gabata. Kamfanin ya kara da cewa jirgin yana kan hanyarsa ta zuwa birnin Lagos cibiyar kasuwancin tarayyar Najeriya daga tashar jiragen ruwa na Port Harcourt a lokacinda yan bindiga suka fadawa jirgin suka kuma tafi da mutane 12 cikin 19 da suke cikin jirgin. 

Amma majiyar ma'aikatar harkokin wajen kasar Swizland ta bayyana cewa babu ko da daya daga cikin wadanda aka sacen dan kasar ta Swizland. 

Satan mutane musamman yan kasashen waje a cikin ruwan tekun da ke kudancin Najeriya don karban kudaden fansa ya zama ruwan dare a yankin Naija Delta na tarayyar Najeriya.