Ivory Coast: An Girke Jami'an Tsaro A Yankin Abobo
Rahotanni daga kasar Ivory Coast na cewa a jiye an girke jami'an tsaro dauke da kayan yaki a yankin Abobo da ke arewacin birnin Abijan, babbar cibiyar tattalin arzikin kasar.
Shafin yada labarai na Afrik Time ya bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron sun wannan yanki ne tun jiya, bayan da samu bayani kan bullar wasu masu dauke da makamai a yankin da suke kai hari kan jama'a, musamman ma wadanda ke kan hanyar zuwa birnin Abijan.
Rahoton ya ce masu dauke da makaman matasa ne zaune gari banza, wadanda suke gallaza wa jama'a, da ufin haddasa wani sabon tashin hankali na kabilancia kasar, an bata kashi tsakanin jami'an tsaron kasar ta Ivory Coast da matasan, inda aka kashe daya daga cikinsu, amma yanzu dai kura ta lafa a yankin.