Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Ya Ziyarci Jihar Kogi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33329-mataimakin_shugaban_kasar_najeriya_ya_ziyarci_jihar_kogi
Mataimakin shugaban kasa a tarayyar Najeriya ya jajantawa mutanen jihar Kogi saboda ambaliyar ruwa da ta halaka mutane akall 108 a yayinda wasu 141,369 suka kauracewa gidajensu.
(last modified 2018-09-25T08:08:28+00:00 )
Sep 25, 2018 08:08 UTC
  • Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Ya Ziyarci Jihar Kogi

Mataimakin shugaban kasa a tarayyar Najeriya ya jajantawa mutanen jihar Kogi saboda ambaliyar ruwa da ta halaka mutane akall 108 a yayinda wasu 141,369 suka kauracewa gidajensu.

Jaridar Punch ta Najeriya tanakalto mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo wanda ya sami rakiyar gwamnatin jihar Kogi Alhaji Yahyah Bello zuwa wurare da ambaliyar ta shafa yana cewa tuni ya bada umurnin a kawo taimakon gaggawa don tallafawa wadanda abin ya shafa. 

Osinbajo ya ziyarci sansanin yan gudun hijira ta St.Luke’s Internally Displaced Persons’ Camp da ke koton-karfe ya ce gwamnatin tarayyar kasar zata yi duk abinda zata iya don kyautta rayuwar mutanen musamman bayan wannan musibar. 

Hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA ta bada sanarwan cewa mutane kimani dubu 441,251 ambaliyar ruwan ta jihar Kogi ta shafa a kananan hukumomi 50 a duk fadin kasar a wannan shekara.