Wasu 'Yan Gudun Hijira Sun kai Farmaki Kan Ofishin MDD A Mauritania
Wasu 'yan gudun hijira sun kai farmaki kan ofishin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya a kasar Mauritania.
Shafin yada labarai na Sahara Media ya bayar da rahoton cewa, daruruwan 'yan gudun hijira ne suka kai farmaki kan ofishin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya da ke birin Nouakchott fadar mulkin kasar, bayan da suka fusata a kan rashin kulawa da wasu bukatunsu.
Rahoton ya ce mutanen sun killace ofishin baki daya, kuma sun hana dukkanin ma'aikatan wurin fita, duk kuwa da cewa ba su cutar da ma'aikatan ba, amma dai sun yi ta hargowa da kuma nuna bacin ransu kan abin da suka kira nuna halin kula da hukumar ke yi dangane da halin da suke ciki.
Daga bisani jami'an tsaron gwamnatin Mauritania sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa mutanen, tare da kame wasu daga cikinsu.