Burundi Ta Dakatar Da Ayyukan Kungiyoyin Kasashen Waje
Mahukuntan Burundi, sun sanar da dakatar da ayyukan kungiyoyin kasashen waje a cikin kasar, har zuwa lokacin da suka fara aiki da sabuwar dokar data tanadi sanya ido ga ayyukansu.
A wata sanarwa da ya karanto a gidan talabijin din kasar, sakataren majalisar tsaron kasar ta (CNS), janar Sisas Ntigurirwa, ya ce bayan bibiyar ayyukan kungiyoyin dake aiki a Burundi, an gano cewa mafi yawansu basa bin doka.
A don haka majalisar tsaron kasar ta dau matakin dakatar da ayyukan kungiyoyin har na tsawan wata ukku daga ranar 1 ga watan Oktoba mai shirin kamawa na 2018.
Ana da dai fargaba akan wannan matakin, zai iya sa kungiyoyin kasashen wajen su kawo karshen ayyukansu a kasar, alhali mafi yawan tallafin kungiyar tarayya Turai na bi ta hannunsu ne.
Burundi dai ta fada cikin rikicin siyasa ne tun bayan da shugaba Pierre Nkurinziza, ya bayyana anniyarsa ta sake tsayawa takara a karo na ukku, a watan Afrilu na 2015, wanda kuma sake zabensa a watan Yuli na shekarar, ya janyo tashin hankalin da ya yi sanadin mutuwar mutane kimanin 1,200