An cafke Jagoran Kungiyar Islama Ta Ansaru A Najeriya
Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da cafke jagoran kungiyar islama ta Ansaru dake da alaka da kungiyar boko haram da kuma Al'Qaida reshen kasashen larabawa ta Aqmi.
Sanarwar ta ce an cafke Khalid al-Barnawi a ranar Juma'a data gabata a wani samame da jami'am tsaron kasar suka kadamar a garin Lokoja dake jihar Kogi a tsakiyar kasar.
wannan dai a cewar kakakin rundinar sojin kasar babban ci gaba a yakin da kasar keyi da ta'adanci.
Rundinar sojin kasar ta ce Khalid al-Barnawi na a sahun gaba a cikin jerin 'yan ta'adan da take nema ruwa a jallo.
ko baya haka al'barnawi na cikin jerin 'yan ta'ada na duniya da Amurka ke nama ruwa a jallo da suka hada da Abubakar Shekau jagoran kungiyar Boko Haram, da Abubakar Adam Kambar wanda ya kirkiro kungiyar Ansaru da kuma Kahalid al barnawi wanda ya dauki jagoranci kungiyar bayan hallaka kambar a wani harin sama da aka kai mabuyar sa a Kano dake arewa Najeriya a watan Maris na shekara 2012