Faransa Na Da Hannu Wajen Durkusar Da Guinea, Inji Alpha Conde
Shugaba Alpha Conde na Guinea, ya dora alhakin rashin ci gaba da kasar ke fuskanta tun bayan samun yancin kai ga halayen kasar Faransa na waccen lokacin.
A wata hira da tashar talabijin ta TV5 da rfi da kuma le jaridar le Monde, kwanaki biyu kafin zagayowar cika shekaru 60 da samun yancin kai na kasarsa, shugaba Conde ya ce Faransa ita ce ummul aba'isin rashin ci gaban kasarsa ta fuskar tattalin arziki.
Kasar Guinea dai ita ce wata kasa Afrika a kudu da hamadar sahara renon Faransa data fara samun yancin kai a shekarar 1958.
Mista Conde ya kara da cewa ya kamata 'yan Faransa su sani cewa, idan kasarsa ta kasa samun ci gaba akwai hannun tsaffin shuwagabanninta, amma ya kamata kuma magabatan Faransa na waccen lokacin, su san suma akwai hannunsu.
Duk da arzikin karkashin kasa da Allah ya hore mata, sama da rabin al'ummar kasar Guinea na rayuwa ne a cikin talauci, a cewar MDD.