Somaliya: An Kashe 'Yan Ta'addar Kungiyar al-Shabab Biyar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33428-somaliya_an_kashe_'yan_ta'addar_kungiyar_al_shabab_biyar
Tashar talabiin din Skynews ta ambato kwamandan sojojin Somaliya Yufus Husain Usman na cewa;Sojojin wannan kasar sun kai farmaki a yankin Kismao inda su ka kwato wasu yankuna daga ikon kungiyar al-shabab.
(last modified 2018-10-01T12:47:00+00:00 )
Oct 01, 2018 12:47 UTC
  • Somaliya: An Kashe 'Yan Ta'addar Kungiyar al-Shabab Biyar

Tashar talabiin din Skynews ta ambato kwamandan sojojin Somaliya Yufus Husain Usman na cewa;Sojojin wannan kasar sun kai farmaki a yankin Kismao inda su ka kwato wasu yankuna daga ikon kungiyar al-shabab.

Usman ya kara da cewa; A yayin farmakin sojojin kasar sun yi nasarar kashe 'yan kungiyar ta al-shabab guda biyar tare da jikkata wasu da dama.

Kungiyar al-shaba tana kai hare-hare a cikin kasar Somaliya da su ka hada da babban birnin kasar Magadishu, haka nan kasashen makwabta. A shekarun baya kungiyar ta shimfida ikonta a cikin sassa daban-daban na kasar, sai dai sojojin gwamnati sun yi nasarar fatattakarsu.

A cikin watan Oktoba na 2017 kungiyar ta kashe mutane 358 da jikkkata wasu 228 a cikin birnin Magadishu kadai.