An Kashe Mutane 20 A Rikicin Kabilanci A Kasar Habasha
(last modified Mon, 01 Oct 2018 19:04:10 GMT )
Oct 01, 2018 19:04 UTC
  • An Kashe Mutane 20 A Rikicin Kabilanci A Kasar Habasha

Mutane akalla 20 ne aka tabbatar da mutuwarsu a rikicin kabalincin da ya auku a tsakanin kabilu a yammacin kasar Habasha

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya nakalto Negeri Lencho jami'i mai kula da harkokin yada labarai na Lardin Oromia daga kudancin kasar yana cewa mutane 20 ne suka tabbatar da mutuwarsu a rikicin kabilancin da ya auku a lardin a cikin makon da ya gabata, sannan wasu dubu 60 kuma suka kauracewa gidajensu. 

Lencho ya kara da cewa mai yuwa yawan wadanda suka mutu ya karu don har yanzun basa da cikekken labarin rikicin da ya faru a wasu kauyuka a cikin lardin. 

Gwamnatin kasar Habasha ta bayyana cewa wasu yan bindiga yayan wata kungiya da ake kira "Sojojin neman 'yencin Oromia" suka haddasa rikici a yankin. Tun cikin watan mayu na shekara ta 2017 ne aka fama da rikici a yankin na Oromo wanda ya kai ga rasa rayuka da dukiyoyi masu yawa, sannan jami'an tsaro sun kama mutanen da dama.