Guinea Na Bikin Cika Shekara 60 Da Samun 'Yancin Kai
Oct 02, 2018 07:53 UTC
Yau, Guinea, ke bikin cika shekaru 60 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Faransa.
Guinea ta samu yancin kai ne a ranar 2 ga watan Oktobar shekarar 1958, kuma ita ce wata kasa a yankin kudu da hamadar sahara data fara samun 'yancin kai daga turawa 'yan mulkin mallaka.
A jawabin da ya gabatar a jajibirin bikin na yau, shugaban kasar Alpha Conde ya nemi 'yan kasar dasu kara hadin kai da kaunar juna.
Shugabannin Afrika da dama daga yankin na halartar bikin da suka hada da Denis Sassou Nguesso na Congo, da Ibrahima Boubacar Kéita na Mali, da Idriss Déby Itno na Chadi da Roch Marc Christian Kaboré na Burkina da Isoufou Mahamadu na Nijar, wandanda zasu halarci faretin sojoji.
Tags