Malamman Addini Na G5 Sahel Na Taro A Mauritania
Oct 04, 2018 15:22 UTC
Jagororin malamai da sarakunnan gargajiya na kungiyar kasashen gungun G5 Sahel, na taro a birnin Nouakchot na kasar Mauritania, kan yaki da tsatsaran ra'ayin addini.
taron dake samun tallafin kungiyar kasashen Turai, na zuwa ne a daidai lokacin da tsatsauran ra'ayin addinin islama ta hanyar wasu haramtatun kungiyoyi ke kara kamari a yankin na Sahel.
Mahalarta taron daga kasashen yankin zasu maida hankali wajen jan hankalin matasa akan kaurace wa kiraye kirayen ire wadannan kungiyoyin musamman Boko Haram dake zaman babbar barazana a yankin.
Kungiyar Boko Haram dai na amfani da matasa wajen yada muggan akidunta da kuma kai hare hare ta'addanci a kasashen Najeriya, Nijar Kamaru da Chadi.
Tags