An Kashe Mutane 8 A Wani Harin Ta'addanci A Borkina Faso
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33488-an_kashe_mutane_8_a_wani_harin_ta'addanci_a_borkina_faso
Ma'aikatar tsaro ta kasar Borkina Faso Ta Bada Sanarwan Mutuwar mutane 8 a wasu hare-haren ta'addanci guda biyu da yan ta'adda suka kai a cikin kasar.
(last modified 2018-10-05T06:34:15+00:00 )
Oct 05, 2018 06:34 UTC
  • An Kashe Mutane 8 A Wani Harin Ta'addanci A Borkina Faso

Ma'aikatar tsaro ta kasar Borkina Faso Ta Bada Sanarwan Mutuwar mutane 8 a wasu hare-haren ta'addanci guda biyu da yan ta'adda suka kai a cikin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya nakalto majiyar ma'aikatar tsaron kasar tana fadar haka a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa a hare-haren da yan ta'adda suka kai a garin Soum daga gabacin kasar jami'an tsaro 8 ne suka rasa rayukansu. 

Labarin ya kara da cewa da farko wata motar Jami'an tsaro ce ta taka nakiya wanda aka bisne a kan hanyarta a ranar Laraban da ta gabata, inda a nan take jami'an tsaro 7 suka rasa rayukansu a yayinda wasu biyu suka ji ranin.

Sai kuma a hari na biyu yan ta'addan da kansu ne suka kai hari kan wani wurin hakar ma'adinai a garin na Soum a jiya Alhamis inda a nan ma suka kashe jami'in tsaro guda.