Jam'iyyar PDP Ta Zabi Atiku A Matsayin Dan Takararta A Zaben 2019
Jam'iyyar PDP a Nijeriya ta zabi tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasar da za a gudanar a a watan Fabrairun 2019 wanda ake ganin zai zama shi ne babbar wanda zai kalubalancin shugaban kasar Muhammadu Buhari wanda shi ma jam'iyyarsa ta APC ta tsayar da shi a matsayin dan takararta.
Rahotanni daga birnin Fatakwal na jihar Rivers inda aka gudanar da zaben sun bayyana cewar wakilai sama da 3,200 daga jihohin Nijeriya 36 ne suka hallara domin zabar dan takarar inda bayan kuri'ar da aka kada aka sanar da Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takarar jam'iyyar ta PDP bayan nasarar da ya samu a kan sauran abokan takararsa 11 da kuri'u 1532.
Sauran 'yan takarar da suka fafata da Atiku Abubakar din sun hada da: Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal wanda ya zo na biyu da kuri'u 693 sai kuma kakakin majalisar dattawan Nijeriyan Bukola Saraki wanda ya zo na uku da kuri'u 317 sai kuma toshon gwamnan jihar Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya zo na hudu da kuri'u 158.
Sauran kuma sun hada da gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwabo da kuri'u 111, sai kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido da kuri'u 96, sai tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmed Markafi da kuri'u 74, sai kuma Turaki Taminu da kuri'u 65 sai tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa da kuri'u 48 sai tsohon kakakin majalisar dattawan Nijeriyan David Mark da kuri'u 35, sai tsohon gwamnan jihar Flato Jonah Jang da kuri'u 19 sai kuma na karshensu Datti Baba Ahmad mai kuri'u 5.