Ana Zaman Makoki A D.R Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33524-ana_zaman_makoki_a_d.r_congo
A Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo, ana zaman makoki na kwanaki uku bayan mummunan hatsarin tankai mai da ya yi sanadin mutuwar mutum akalla 60.
(last modified 2018-10-08T07:46:27+00:00 )
Oct 08, 2018 07:46 UTC
  • Ana Zaman Makoki A D.R Congo

A Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo, ana zaman makoki na kwanaki uku bayan mummunan hatsarin tankai mai da ya yi sanadin mutuwar mutum akalla 60.

Shugaban kasar Joseph Kabila, ya mika sakon ta'aziyarsa ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa dasu da kuma fatan sauki wa wadanda suka jikkata.

Hadarin dai ya auku ne ranar Asabar data gabata gaf da garin Kisantu, akan babbar hanyar dake sada birnin Kinshasa da babbar tashar ruwan kasar ta gabar tekun Atlantic dake garin Matadi.

Akalla mutane 60 ne suka gamu da ajalinsu kana wasu kimanin dari suka jikkata ta hanyar konewa, sakamakon taho mu gama tsakanin tankar ta mai da wata mota, a yammacin kasar ta DR Congo.