Oct 09, 2018 06:48 UTC
  • Maroko: 'Yan ci-Rani Fiye Da 600 Sun Tsira Daga Halaka

Sojan ruwan kasar Maroko ne su ka sanar da tseratar da 'yan ci-rani 615 daga nustewa a cikin ruwa a ckin tekun Mediterranea

"Yan ci ranin da su ke a cikin kananan kwale-kwale 31 suna kan hanyarsu ne ta shiga cikin kasar Spain, domin isa sauran kasashen turai.

Sojojin ruwan na kasar Morokon sun ce dukkanin mutanen da su ka tseratar da su suna nan cikin koshin lafiya.

A ranar 1 ga watan Oktoba wani kwale-kwale mai dauke da mutane da dama ya nutse a gabar ruwan Moroko wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 13, yayin da masu kamun kifi su ka tseratar da wasu 30.

Wata kididdiga ta Majalisar Dinkin Duniya ta ambaci cewa; Daga farkon wannan shekarar zuwa yanzu adadin 'yan ci-ranin da su ka halaka a cikin tekun meditrranea sun kai 1700.

Tags