Sep 06, 2018 11:53 UTC
  • Yara Yan Gudun Hijira Kimani 10 Ne Suke Kasar Espaniya A Halin Yanzu.

Ministan kiwon lafiya na kasar Espaniya ya bada sanarwan cewa akwai yara kanana da matasa yan kudun hijira kimani dubu 10 a cikin kasar a halin yanzu.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalti ministan yana fadar haka a birnin Madrid ya kara da cewa ko a jiya laraba yara kanana da matasa kimani 49 suka shigo kasar daga kasar Morocco. Matsalolin rayuwa wadanda suka hada da yake yake da yunwa da kuma rashin aikin yi na daga cikin dalilan rabuwar wadanda yara da iyayensu a kasashen Afrika.

A bisa dokokin kasar Espaniaya dai idan wadannan yara suka zauna na shekaru biyu a kasar sun cancani a basu shaidar zama dan kasa. 

Tags