Ma'aikatan Filin Jirgin Sama A Lagos Sun Yi Barazanar Fadada Yajin Aikin
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33570-ma'aikatan_filin_jirgin_sama_a_lagos_sun_yi_barazanar_fadada_yajin_aikin
Kungiyar ma'aikatan tashar jiragen sama ta Murtala Mohammad a birnin Lagos a Najeria ta yi barazanar fadada yajin aikin da take yi saboda korar wasu abokan aikinsu wanda hukuma mai kula da tashar jiragen saman ta yi.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Oct 11, 2018 19:02 UTC
  • Ma'aikatan Filin Jirgin Sama A Lagos Sun Yi Barazanar Fadada Yajin Aikin

Kungiyar ma'aikatan tashar jiragen sama ta Murtala Mohammad a birnin Lagos a Najeria ta yi barazanar fadada yajin aikin da take yi saboda korar wasu abokan aikinsu wanda hukuma mai kula da tashar jiragen saman ta yi.

Jaridar Punch ta Najeriya ta bayyana cewa yayan kungiyar sun fito jerin gwano a safiyar Alhamis a Taminal ta MMA2 a tashar jiragen inda suke kira ga "Bi-Courtney Aviation Services Limeted" BASL ta dawo da abokan aikinsu 24 da ta kora saboda suna sun manya manyan kungiyoyin zirga-zirgan jiragen sama na kasar sun dunkule su samar da kungiya kula don bin hakkokinsu. 

Mataimakin babban sakataren kungiyar ma'aikatan Mr Frances Akinjole ya fadawa kamfanin dillancinn labaran Najeriya NAN kan cewa mutanensa zasu rufe sauran wuraren shiga jiragen sama da suke aiki idan har hukumar BASL ta yi kunnen uwan shegu da bukatansu. 

Akinjole ya ce kungiyarsa ta yi kokarin sasantawa da hukumar BASL amma ba tare da samun nasara ba, don haka ba wata hanyar da ta rage masu inda banda shiga yajin aiki da kuma jerin gwano da suke yi. 

Jami'an tsaro sun killace wurare da dama a tashar jiragen saman don tabbatar da zanga-zangar bata zama ta tashin hankali ba.