Ana Zaben Kananen Hukumomi A Ivory Coast
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33595-ana_zaben_kananen_hukumomi_a_ivory_coast
Yau Asabar al'ummar Ivory Coast sama da miliyan shida da sukayi rejista ke kada kuri'a a zabukan wakilan kananan hukumomin kasar.
(last modified 2018-10-13T08:21:25+00:00 )
Oct 13, 2018 08:21 UTC
  • Ana Zaben Kananen Hukumomi A Ivory Coast

Yau Asabar al'ummar Ivory Coast sama da miliyan shida da sukayi rejista ke kada kuri'a a zabukan wakilan kananan hukumomin kasar.

Yan takara dubu ashirin da biyu ne ke takara a zaben, saidai jam’iyyar tsohon Shugaban kasar Laurent Gbagbo dake tsare a kotun ICC ta kaucewa zaben.

Ana dai ganin zaben zai kasance zakarin gwajin dafi wa hukumar zaben kasar a zaben Shugaban kasar na shekara ta 2020.