AFCON 2019: Najeriya Ta Doke Libya Da Ci 4 - 0
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33615-afcon_2019_najeriya_ta_doke_libya_da_ci_4_0
A ci gaba da buga wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin kwallin kafa na kasashen Afrika AFCON, Najeriya ta lallasa Libya da ci 4 - 0 a wasan da suka buga jiya a garin Uyo na jahar Akwa Ibom a Najeriya.
(last modified 2018-10-14T07:32:00+00:00 )
Oct 14, 2018 07:32 UTC
  • AFCON 2019: Najeriya Ta Doke Libya Da Ci 4 - 0

A ci gaba da buga wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin kwallin kafa na kasashen Afrika AFCON, Najeriya ta lallasa Libya da ci 4 - 0 a wasan da suka buga jiya a garin Uyo na jahar Akwa Ibom a Najeriya.

Shafin yada labarai na jaridar Vanguard ta Najeriya ya bayar da rahoton cewa, fara wasan ke da wuya a cikin kasa da mintuna hudu, Najeriya ta samu bugun daga kai sai gola, inda Odion Ighalo ya saka kwallo ta farko.

An tafi hutun rabin lokaci ba tare da Libya ta iya farkewa ba, yayin da ita ma Najeriya ba ta iya kara saka wata kwallo ba.

Bayan dawowa hutun rabin lokaci, Najeriya ta kara zura kwallaye uku, inda Odion Ighalo ya kara biyu, Samuel Kalu kuma ya zura guda daya, wanda hakan ya baiwa Najeriya nasara da ci 4 - 0.

A ranar 16 ga watan Oktoba ne za a yi karawa ta biyu tsakanin Najeriya da Libya a kasar Tunisia.

Yanzu haka dai Najeriya tana da maki 6, bayan da ta ci wasannin biyu a jere.