Burkina Faso : Karon Farko An Kafa Mutum-mutumin Sankara
(last modified Mon, 15 Oct 2018 18:18:48 GMT )
Oct 15, 2018 18:18 UTC
  • Burkina Faso : Karon Farko An Kafa Mutum-mutumin Sankara

A Burkina Faso, a karon farko an aza tubalin da za'a kera mutum mutumin martaba tsohon shugaban kasar mirigayi Thomas Sankara, a Ouagadugu babban birnin kasar.

Dubban 'yan kasar ne ciki har da 'yan siyasa suka halarci bikin aza tubalin kafa mutum mutumin.

Wannan dai na zuwa ne a yayin zagayowar cika shekaru 31 cif da kisan Sankara din wanda ya jagoranci gwagwarmayar  samarwa da 'yan kasar 'yanci a fagage da dama na rayuwa.

Mutum mutimin mai tsawan mita 5 za'a gina shi ne a dandalin cibiyar kasar ta gwagwarmaya inda a nan ne aka kashe Sankara a ranar irin ta yau 15 ga watan Oktoba 1987 a wani juyin mulki wanda amininsa kuma abokin aikinsa Blaise Campaore ya shirya.

An dai shafe kusan shekaru 27 ana neman haske kan kisan Sankara saidai hakan bata yi ba a lokacin mulkin Blaise Compaure.

Daga bisani dai a shekara 2014, Blaise Compaure ya bar mulki a ranar 31 ga watan Oktoba sakamakon boren jama'ar na kin jinin gwamnatinsa.