Fashewar Botutun Mai Da Gobara Ya Halaka Mutane 60 A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33642-fashewar_botutun_mai_da_gobara_ya_halaka_mutane_60_a_najeriya
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa wani bitutun man fetura ya fashe sannan ya kama da wuta a yankin gabacin jihar Abia daga kudancin tarayyar Najeriya a ranar jumma'a da ta gabata.
(last modified 2018-10-16T06:31:30+00:00 )
Oct 16, 2018 06:31 UTC
  • Fashewar Botutun Mai Da Gobara Ya Halaka Mutane 60 A Najeriya

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa wani bitutun man fetura ya fashe sannan ya kama da wuta a yankin gabacin jihar Abia daga kudancin tarayyar Najeriya a ranar jumma'a da ta gabata.

Labarin ya kara da cewa da farko mutane 24 suka rasa rayukansu, amma daga baya wannan adadin ya karu zuwa 60, sannan har yanzun wasu na jinya sanadiyar kuna da suka samu saboda gobarar da ta taso bayan fashe bututun. Jami'an kamfanin man fetur na kasar wato NNPC sun dora laifi a kan barayin da suke fasa bututun man don sata.

Kamfanin ya kara da cewa a halin yanzu dai sun dakatar da kwararar mai a cikin bututun, sun kuma sami nasarar kashe gobarar. Banda haka sun fara aikin gyaran butitun don ya ganin ya dawo aiki nan ba da dadewa ba. Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA da ke yankin ta tabbatar da labarin ta kuma kara da cewa mai yuwa a kara samun wadanda zasu rasa rayukansu.

A ranar 12 ga watan mayun shekara ta 2006 ma barayi sun fasa wani bututun mai a kusa da birnin Lagos daga kludancin kasar, inda gobara da tashi ta kuma yi sanadiyyar tuwar mutane 150.