Gwamnatin Najeriya Ta Ce Ta Yi Duk Kokarinta Don Ceto Hauwa
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ta yi duk abinda yakamata ta yi don kubutar da ran Hauwa daga hannun Boko Haram, amma kungiyar ta kashe ta.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya nakalto ministan watsa labarai Alhaji Lai Mohammad yana fadara haka a jiya Litinin ya kuma bayyana damuwarsa da yadda kungiyar ta kashe Hauwa Mohammad Liman tare da duk kokarin da ta yi don kubutar da ita.
A wani bayani wanda ministan ya fitar a birnin Lodon inda yake ziyarar aiki ya ce babu wani abinda zai halatta zaban da jinin mutanen da basu san hawa ko sauka ba.
Lai ya kara da cewa tun bayan kamata sun sanar da kungiyar kan cewa kofar tattaunawa don sakinta a bude yake, don haka kisanta ya zo masu ba zata. Lai ya mika ta'aziyyarsa ga iyaye da iyalan Hauwa Mohammad Liman wacce kungiyar Boko Haram ta bada sanarwan kisanta. Hauwa dai ita ce jami'ar bada agaji wacce take aiki a sansanin yan gudun hijira a jihar Borno wacce kungiyar boko haram ta sace sannan ta kashe daga baya.
Lai ya godewa duk wadanda suke kokari don ganin an kubutar da rayuwar mutanen da ake sacewa tare da bukatu daban daban a kasar.