Najeriya : Yan Sanda Da EFCC Basa Da Labarin Bidiyon Ganduje
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33645-najeriya_yan_sanda_da_efcc_basa_da_labarin_bidiyon_ganduje
Jami'an 'yansanda da hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa sun ce ba sa da labarin hotunan bidiyo da aka yada a jaridu da kuma kafafen sadarwa da gwamnan jihar Kano Umar Ganduje yana karban rashawa a hannun wasu kamfanonin da suke masa aiki a Kano.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Oct 16, 2018 06:33 UTC
  • Najeriya : Yan Sanda Da EFCC Basa Da Labarin Bidiyon Ganduje

Jami'an 'yansanda da hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa sun ce ba sa da labarin hotunan bidiyo da aka yada a jaridu da kuma kafafen sadarwa da gwamnan jihar Kano Umar Ganduje yana karban rashawa a hannun wasu kamfanonin da suke masa aiki a Kano.

Jaridar Premiumtimes ta Najeriya ta bayyana cewa a lokacinda wakilinta ya tuntubi Wilson Uwujaren kakakin hukumar EFCC a jiya ya ce har yanzun ba su da masaniya kan wadannan hotunan Vedio wadanda jaridar Daily Nigeria ta watsa kafin ya je ko ina a shafuffukan sadarwa ta Internet. Hotunan dai suna nuna gwamnan Jihar Kani dan jam'iyyar maim mulki APC yana karban cin hanci da rashawa a hannun wasu kanfanonin da suke masa aiki a jihar.

Jaridar Daily Nigeria ta ce tana da irin wadannan hotunan na Umar Ganduje guda 15 wadanda aka dauka a cikin watanni, sannan zasu watsa su daya bayan daya.

Hakama kwamishinan 'yansanda na jihar Kano Rabiu Yusuf, ya ce har yanzun bai ga hotunan ba, amma idan ya gani zai fadawa yan jaridu matsayin hukumarsa. 

Jaridar Daily Nigeria ta ce shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ga hotunan sannan ya bada umurnin a kafa komitin bincike. Sai kuma majalisar dokokin jihar Kano ita ma jaridar tace ta kafa komitin binciken gaskiyar labarin. 

Gwamnonin a Nageriya dai suna da rigar kariya daga gurfana a gaban kuliya sai idan har majalisar dokokin jihar ce ta dauki mataki a kansa.

Gwamnatin jihar kano ta bayyana cewa zata kai kara a gaban kotu kan wannan cin mutuncin da aka yiwa gwamnan