INEC : Jam'iyyu 17 Kacal Suka Mika Sunayen Yan Takararsu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33677-inec_jam'iyyu_17_kacal_suka_mika_sunayen_yan_takararsu
Hukumar zabe mai zaman kanta a tarayyar Najeriya ta bada sanarwan cewa jam'iyyu 17 ne kadai daga cikin jam'iyyu 91 suka bada sunayen yan takararsu na zaben shekara ta 2019 a zuwa yau 18 ga watan Octoba.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Oct 18, 2018 12:17 UTC
  • INEC : Jam'iyyu 17 Kacal Suka Mika Sunayen Yan Takararsu

Hukumar zabe mai zaman kanta a tarayyar Najeriya ta bada sanarwan cewa jam'iyyu 17 ne kadai daga cikin jam'iyyu 91 suka bada sunayen yan takararsu na zaben shekara ta 2019 a zuwa yau 18 ga watan Octoba.

Jaridar Premuimtimes ta nakalto shugaban hukumar zaben Mahmoddd Yakubu yana fadar haka a jiya Laraba. Ya kuma kara da cewa hukumar ta na tsammanin zata karbi sunayen yan takara daga jam'iyyu masu yawa a makon da ya gabata, ganin cewa lokacin rufe karban sunayen ya karato, amma hakan bai faru ba. 

Sashi na 31 (1) a dokar hukumar zabe ta shekara ta 2010 wacce aka yi wa koskorima ta ambaci cewa dole ne jam'iyyun siyasa su mika sunayen yan takara kwanaki 60 kafin babban zabe.

Yakubu ya kara da cewa ana bukatar hukumar ta buga sunayen dukkan yan takara da ta karbi sunayensu da kuma takarunsu makooni biyu bayan karbansu. Daga karshe shugaban hukumar zaben ya bayyana cewa ba ya son a zo masa da sunayen yan takara a kurerren lokaci, don hakan zai iya rikita ayyukansu. 

Har'ila yau hukumar zaben ta ce majalisar dokokin kasar ta amince da Naira billiyon 189 da hukumar ta bukata don gudanar da zaben na shekara ta 2019.