Gabon : 'Yan Adawa Sun Ce An Tabka Magudi A Zaben 'Yan Majalisa
Manyan jam'iyyun adawa a Gabon sun yi zargi jam'iyya mai mulki a kasar da tabka magudu a zaben 'yan majalisar dokokin dana wakilan kananan hukumomin kasar da aka kada kuri'arsa a ranar 6 ga watan Oktoban nan.
Da yake bayyana hakan jagoran jam'iyyar adawa ta (RHM), Alexandre Barro Chambrier ya ce an tabka kura kurai masu yawa, sannan jam'iyya mai mulki ta yi amfani da kudi don samun kuri'a da kuma murde sakamakon zabe a wasu sassan kasar.
Shi ma dai a wani taron manema labarai shugaban jam'iyyar adawata UN, Zacharie Myboto, ya ce an tafka kura kurai da dama a zaben.
Saidai masu sanya ido a zaben na kungiyar tarayya Afrika ta (AU), ta yada da yadda zaben ya gudana ba tare da samun matsaloli ba, lamarin da 'yan adawan suka ce abun takaici ne halartan nasu domin sanya ido a zaben.
Jam'iyyar mai mulki ta kasar dai PDG, ta samu gagarimin rinjaye a zaben 'yan majalisar zagayen farko.
A ranar 27 ga watan Oktoban nan ne za'a je zagaye na biyu domin cike gurbin kujeru 26 da suka rage a cikin 143 da majalisar dokokin kasar ta kunsa.