Kotu Ta Daure Jagoran 'Yan Adawa A Benin
Kotu a Jamhuriyar Benin ta yanke wa jagoran ‘yan adawar kasar kuma hamshakin dan kasuwa Sebastien Ajavon hukuncin daurin shekaru 20 A a gidan yari bayan samunsa da laifin fataucin miyagun kwayoyi duk da cewa ya gudu zuwa kasar Faransa.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa wata kotu a kasar Benin ta yanke hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari ga jagoran ‘yan adawar kasar kuma hamshakin dan kasuwa Sebastien Ajavon wanda ya taimaka wa shugaban kasar mai ci Patrice Talon samun nasara a zaben 2016, kotun wanda ta yi zamanta a birnin Porto Novo dake babban birnin kasar ta fitar da sammacin kasa da kasa domin taso keyarsa zuwa gida daga Faransa inda yake zaune yanzu haka.
Da dama daga cikin yan siyasa a kasar ta Benin suka fara bayyana damuwarsu tareda da tofin Allah tsine ga wannan kudiri da hukumomin kasar suka dauka.