Rikicin Kaduna: Buhari Ya Bukaci Mutane Su Zabi Zaman Lafiya Tare
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33718-rikicin_kaduna_buhari_ya_bukaci_mutane_su_zabi_zaman_lafiya_tare
Shugaban Mohammadu Buhari na tarayyar Najeriya ya bukaci yan najeriya su koyi zama tare da hakuri da juna, don tashin hankali a ko yauce ba zai taba zama dai-dai da zaman lafiya ba.
(last modified 2018-10-21T06:23:44+00:00 )
Oct 21, 2018 06:23 UTC
  • Rikicin Kaduna: Buhari Ya Bukaci Mutane Su Zabi Zaman Lafiya Tare

Shugaban Mohammadu Buhari na tarayyar Najeriya ya bukaci yan najeriya su koyi zama tare da hakuri da juna, don tashin hankali a ko yauce ba zai taba zama dai-dai da zaman lafiya ba.

Kamfanin dillancin labaran NAN na gwamnati Najeriya ya nakalto shugaban yana fadara haka a lokacinda yake magana dangane da rikicin da ya auku a ranar jumma'a da ta gabata a kasuwar magani a birnin kaduna.

Shugaban ya nuna damuwarsa ta yadda mutanen kasar suke komawa ga zubar da jinin junansu sanadiyyar karamar matsala wacce ana iya warwareta a cikin ruwan sanyi.

Shugaba Buhari ya kara da cewa babu wani addini ko al-ada da halatta zubar da jin mutane haka kawai. Daga karshe shugaban ya kammala da cewa babu wata al-umma da zata ci gaba a cikin tashin hankali da rashin zaman lafiya.

A wani bangre na jawabin nasa shugaban Buhari ya yabawa gwamnatin Jihar kaduna wacce ta gaggauta daukar mataki don kawo karshen rikicin na kasuwar Magani. 

Wasu rahotanni sun nuna cewa rikicin na kasuwar Magani wanda ya auku a ranar alhamis, wanda ya lakube rayukan mutane 55, ya tashi ne sanadiyyar sabani a tsakanin matasa biyu da suke tura amalanke a kasuwar. 

Kwamishinan yansanda na jihar Kaduna Ahmad Abdurrahman ya bayyana cewa an kama mutane 22 dangane da rikicin. Banda haka gwamnatin jihar kaduna ta kafa dokar hana yawo na sa'oi 24 a unguwar kasuwar Maganin a ranar Jumma'a.