An hallaka wani babban jami'in tsaro a kasar Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3373-an_hallaka_wani_babban_jami'in_tsaro_a_kasar_somaliya
Wasu 'yan bindiga sun bindige wani babban jami'in ma'aikatar leken asiri na kasar Somaliya
(last modified 2018-08-22T06:58:05+00:00 )
Apr 04, 2016 04:11 UTC
  • An hallaka wani babban jami'in tsaro a kasar Somaliya

Wasu 'yan bindiga sun bindige wani babban jami'in ma'aikatar leken asiri na kasar Somaliya

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar China ya nakalto Abdulkadir Muhamad Abdulkadir kwamishinan yankin Hamrawin na kudu maso gabashin Somaliya A Yau Litinin na cewa A jiya Lahadi wasu 'yan bindiga da ba san ko su waye ba sun buda wuta kan motar Muhamad Farah daya daga cikin jami'an ma'aikatar leken asirin kasar,inda suka hallaka shi har lahira.

Abdulkadir ya kara da cewa tuni jami'an 'yan sanda suka fara gudanar da bincike domin gano wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari, saidai ana zarkin kungiyar ta'addancin nan ta Ashabab mai alakar kut da kut da kungiyar Alka'ida domin ta saba kai irin wannan hare-hare kan manyan jami'an kasar.