Wata Tawagar Gwamnatin Amurka Zata Ziyarci Najeriya Da Wasu Kasashen Afrika
Wata tawagar gwamnatin kasar Amurka karkashin jagorancin mataimakin sakataren harkokin wajen kasar mai kula da bangaren Afrika Tibor Nagy zata ziyarci wasu kasashen Afrika daga ciki har da tarayyar Najeriya. Ana saran tawagar zata yi kokarin karfafa dangantakar Amurka ta fuskar kasuwanci da kasashen Afrika a ziyara.
Jaridar Premiumtime ta Najeriya ta nakalto shafin yanar gizo na ma'aikatar harkokin kasar kasar Amurka yana fadar haka a ranar Litinin, ya kuma kara da cewa Mr Nagi zai fara ziyararsa da kasar Britaniya da Faransa.
Sannan kasashen Togo, Guinea da Mali. Mr. Nagi zai yada zangonsa na karshe a tarayyar Najeriya inda ake saran bayan ganawa da jami'an gwamnatin kasar, da kuma yan kasuwar Najeriya zai yi jawabi a jami'ar Baze da ke birnin Abuja, dangane da dangantakar kasuwanci tsakanin Amurka da kasashen Afrika.