Najeriya: Boko Haram Ta Kashe Fararen Hula Biyu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33763-najeriya_boko_haram_ta_kashe_fararen_hula_biyu
Majiyar tsari daga Najeriya ta ce 'yan kungiyar ta Boko Haram sun kashe fararen hula biyu a yankin arewa maso gabacin kasar
(last modified 2018-10-23T15:24:31+00:00 )
Oct 23, 2018 15:24 UTC
  • Najeriya: Boko Haram Ta Kashe Fararen Hula Biyu

Majiyar tsari daga Najeriya ta ce 'yan kungiyar ta Boko Haram sun kashe fararen hula biyu a yankin arewa maso gabacin kasar

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ba da labarin cewa; "Yan ta'addar sun kai hari ne akan kauyen Mifah mai nisan kilo mita 7 daga birnin Chibok a jahar Borno.

Bugu da kari, a yayin harin 'yan kungiyar ta 'ta'addanci sun jikkata wasu mutane shida.

A shekarar 2014 ne kungiyar ta Boko Haram ta sace 'yan mata 200 daga garin Chibok, lamarin da ya fusata al'ummar duniya.

 Daga 2009 zuwa yanzu, kungiyar ta Boko Haram ta kashe mutane fiye da 13,000 a cikin Najeriya da kuma wasu dubban a kasashen makwabta.

Da akwai mutane miliyan daya da 800 ne su ka zama 'yan gudun hijira sanadiyyar rikicin na Boko Haram