Sabuwar Majalisar Tarayyar Afirka Ta Yi Zamanta Na Farko A Birnin Kigali
Oct 23, 2018 18:58 UTC
Zaman Majlisar da aka yi a jiya Litinin ya sami halartar wakilai 275 daga kasashen Afirka 55.
'Yan Majalisar sun tattauna batutuwa daban-daban da su ka shafi nahiyar Afirka da matsalolin da take fuskanta daga cikin hadda batun samar da muhimman cibiyoyi na gwmanati da kuma bunkasa harkokin demokradiyya.
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ne ya gabatar da jawabin bude zaman Majalisar inda ya yi magana akan muhimmancin rawar da Majalisar take takawa. Bugu da kari Kagame ya yi magana akan yadda Majalisar za ta taimaka wajen yi wa kungiyar tarayyar Afirka kwaskwarima.
Shekaru 14 kenan da aka kafa Majalisar tarayyar Afirkan wacce take da manufar warware matsalolin da nahiyar take fuskanta.
Tags