Aljeriya: Wajibi Ne Faransa Ta Biya Diyyar Zamanin Mulkin Mallaka
Wata ' yar majalisar dattijan kasar Aljeriya ce ta bukaci kasar Faransa da ta biya diyyar mulkin mallaka na tsawon shekaru 132
'Yar Majalisar dattijan Louisette Ighilahriz ta zargi Faransa da wawason dukiyar kasar Aljeriya daga 1830 zuwa 1962, don haka wajibi ne ta biya diyya.
Sai dai 'yan Majalisar ta Aljeriya ta ce Faransa ba za ta iya biyan diyyar barnar da ta yi wa Aljeriya ba saboda girman laifukan da ta tafka.
Ana kiran kasar Aljeriya da sunan kasar Shahidai miliyan daya saboda nuna yawan mutanen kasar da mulkin mallakar faransa ya kashe.
Aljeriya ta sami 'yanci ne daga Faransa a 1962. "Yar majalisar dattijai Louisette Ighilahriz tana cikin wadanda su ka yi gwgawarmayar samarwa kasar 'yanci.