Najeriya : An Sassauta Dokar Hana Fita A Kaduna
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33768-najeriya_an_sassauta_dokar_hana_fita_a_kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna a Najeriya ta sanar da sassauta dokar hana zirga zirga ta sa'o'i 24 da aka sanya a jihar ranar Lahadi sakamakon mummunan rikicin kabilanci da ya barke a makon jiya.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Oct 24, 2018 05:54 UTC
  • Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai
    Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai

Gwamnatin jihar Kaduna a Najeriya ta sanar da sassauta dokar hana zirga zirga ta sa'o'i 24 da aka sanya a jihar ranar Lahadi sakamakon mummunan rikicin kabilanci da ya barke a makon jiya.

An sassauta dokar daga awanni 24 zuwa 20 don baiwa al’ummar jihar dama gudanar da harkokinsu.

Gwamnan jihar ne Nasir El-Rufai ya sanar da hakan a shaffinsa na Twetter, bayan da aka kammala wani taron majalisar tsaro ta jihar.

Saidai gwamnatin jihar ta ce ba duka sassan jihar ne ba aka sassauta dokar hana fitar.

Kawo yanzu dai, mutane 78 ne aka tabbatar sun mutu sanadiyyar rikicin da ya barke makon da ya gabata, a jihar ta Kaduna dake arewacin Nijeriya.

An samu karuwar adadin ne bayan jami'ai a jihar sun tabbatar da mutuwar karin mutane 23 da jikkatar wasu 17, sakamakon bazuwar da rikicin ya yi zuwa birnin jihar a ranar Lahadin da ta gabata.