Jaafar Jaafar:Hotunan Bidiyon Na Gwamnan Kano Na Karban Rashawa Ingantattu Ne
Dan jaridan da ya yada hotunan bidiyo na gwamnan kana Alhaji Umar Andullahi Ganduje yana karban rashawa, wato Jaafar Jaafar ya bayyana a gaban komitin bincike na majalisar dokokin jihar Kano a yau Alhamis, inda ya tabbatar da cewa hotunan da ya yada a shafin yanar gizo na jaridar Daily Nigerian a cikin yan makonnin da suka gabata ingantattu ne.
Jaridar Premuimtimes ta Najeriya ta bayyana cewa Jaafar Jaafar ya kara da cewa wani abokinsa daga cikin yan kwangila da sukewa gwamnatin jihar Kano aiko ne ya taimaka masa wajen daukar hotunan.
Kafin haka Jaafar ya ce abokin nasa ya sha yin masa korafi kan cewa gwamnan yana karban kashi 15 zuwa 25% na duk kwangilan da yake basu. Da haka kuma suka amince su dauki hotunan gwamnan yana karban cinhancin ta wata naura daukar hotunan bidiyo wanda aka makala a kan rigarsa.
Jaafar ya kara da cewa kwararro a ma'aikatarsa da na wasu manya manyan kafafen yada labarai a duniya sun tabbatar da ingancin hotunan bidiyon da suka dauka ya yadasu.
Don ganin irin hatsarin wannan fallasar, Jaafar Jaafar ya tabbacin tsaron lafiyasa kafin ya amsa gayyatar komitin bincike na majalisar dokokin jihar ta Kano a yau Alhamis.
Gwamnatin jihar dai ta bayyana cewa hotunan da Jaafar ya yada ba ingantattu bane, kuma har ma sun shigar da kara a gaban kotu don neman a hukunta dan jaridar.