Sudan Ta Kudu : An Sallami Fursunonin Siyasa Da Dama
(last modified Fri, 26 Oct 2018 05:50:51 GMT )
Oct 26, 2018 05:50 UTC
  • Sudan Ta Kudu : An Sallami Fursunonin Siyasa Da Dama

Gwamnatin Sudan Ta Kudu ta sako wasu fursunoni na siyasa da wasu na yaki guda biyar a kokarin da take yi na cika alkawarin da ta dauka cikin yarjejeniyar sulhu na kasar da aka sanya wa hannu a watan da ya gabata.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo wani babban jami'in tsaro na kasar Sudan ta Kudu yana cewar an sako mutane biyar din don cika yarjejeniyar sulhu da aka cimma tsakanin gwamnatin da 'yan tawaye a birnin Addis Ababa babban birnin kasar Ethiopia.

To sai dai wasu majiyoyi sun ce mutanen da aka sako din ba sa daga cikin manyan jami'an babbar kungiyar 'yan tawayen ta Riek Macher, tsohon mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudun kamar yadda yarjejeniyar ta tanada cewa wajibi ne a sako manyan jami'an bangarori biyu da ake tsare da su.

Tun a shekara ta 2013, wato shekaru biyu da kasar Sudan ta Kudun ta sami 'yancin kanta daga kasar Sudan, kasar ta fada cikin rikici musamman bayan rikicin da ya barke tsakanin shugaban kasar Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar lamarin da da ya zuwa yanzu yayi sanadiyyar mutawar sama da mutane 50,000 kana wasu sama da miliyan biyu kuma aka tilasta musu gudun hijira.