Najeriya : An Haramta Amfani Da Jirage Marasa Matuka Ba Da Izni Ba
A kokarin da gwamnatin Nijeriya take yi na tabbatar da tsaro a kasar, gwamnatin ta haramta ajiye bindigogi, amfani da jiragen sama marasa matuka da kuma kayyayakin watsa labarai ba tare da izini ba.
Babban mai ba wa shugaban kasar Nijeriyan shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, ne ya sanar da hakan a wani taron tsaro da aka gudanar a Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya inda ya ce a halin yanzu kafafen watsa labarai na zamani bugu da kari kan mallakar wasu abubuwa irin su jiragen sama marasa matuka da kayayyakin watsa labarai da wasu bangarori da ba na gwamnati ba suke yi sun kasance daya daga cikin manyan hanyoyin da suke barazana ga tsaron Nijeriyan.
Mr. Mungono ya kafa misali da irin rikicin da yake faruwa a jihohin Benue, Flato, Zamfara da Kaduna wanda yace kafafen watsa labarai na zamani sun taka gagarumar rawa wajen rura wutar wannan rikicin ta hanyar yada labarurruka marasa tushe.
Don haka ya shawarci 'yan kasar da su guji mallakar wadannan abubuwa ba tare da izinin hukumomin da abin ya shafa ba, yana mai kiran wadanda suka mallake su da su mika su ga hukumomin tsaron da suka dace, yana mai shan alwashin cewa doka za ta yi aiki kan wadanda suka ki girmama wannan kiran.