Najeriya : An kara Sanya Dokar Ta Baci A Kaduna
Oct 26, 2018 11:22 UTC
Gwamnatin jihar Kaduna a Najeriya ta sanar da sake sanya wata dokar hana zirga-zirga ta sa'o'i 24 a garin Kaduna da kewayensa a yau Juma'a.
Mai magana da yawun gwamnan jihar ne Samuel Aruwan ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook.
Matakin dai a cewar sanarwar ya biyo ne bayan kashe wani basarake Agom Adara a ranar Juma'a wanda aka sace a makon jiya.
A ranar Laraba data gabata da gwamnatin jihar ta sanar sassauta dokar ta bakin da aka kafa a ranar Lahadi data gabata saboda baiwa al'umma damar gudanar da al'amurransu na kasuwanci.
Kafin hakan dai, mutane 78 ne aka tabbatar sun mutu sanadiyyar rikicin da ya barke makon da ya gabata, a jihar ta Kaduna dake arewacin Nijeriya.
Tags