Oct 27, 2018 11:49 UTC
  • Jamus : Kyautata Tattalin  Afrika Ne Zai Dakatar Da Kwararar Yan Gudun Hijira

Waziriyar Kasar Jamus Angela Merkel ta bayyana cewa kyautata tattalin arzikin kasashen Afrika ne kadai zai iya dakatar da kwararar bakin haure daga nahiyar zuwa kasashen turai.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto waziyar kasar ta Jamus, Angela Merkel  tana fadar haka a jiya jumma'a a lokacin da take ganawa da firaiministan jumhuriyar Check, ta kuma kara da cewa dole ne kasashen Turai su yi aiki tare don kyautata tattalin narzikin kasashen Afrika, wanda shi ne kadai hanyar kawo karshen kwararar bakin haure zuwa kasashen nasu.

Waziriyar ta Jamus ta kara da cewa, yan kasashen Afrika, musamman matasa ba za su daina kwarara zuwa kasashen Turai ba sai in har sun sami hanyoyin kyautata rayuwarsu a kasashensu.

A nashi bangaren Firaiministan kasar Jumhuriyar Check ya bayyana cewa zai halarci taron Sicily a tsakiyar watan Nuwamba mai kamawa inda shuwagabannin kasashen Turai zasu tattauna dangane da hanyoyin warware matsalar bakin haure zuwa nahiyar ta Turai. 

 

 

 

Tags