An Tsige Shugaban Majalisar Dokokin Afrika Ta Tsakiya
'Yan majalisar dokokin Jamhuriya Afrika ta tsakiya sun kada kuri'ar tsige kakakin majalisar Abdou Karim Meckassoua, bayan gabatar da bukatar tsige shi bisa zargin karkata kudade da kuma fifita wasu.
Bayan shafe dogon lokaci na tafka muhawara a zauren majalisar, 'yan majalisa 98 ne suka kada kuri'ar yin na'am da tsige shugaban majalisar.
Dama dai kuri'a amincewa 93 ne aka bukata don tsige shugaban majalisar.
Wannan dai shi ne karon farko da irin hakan ta taba faruwa a wannan kasa ta jamhuriya Afrika ta Tsakiya, inda wasu ke danganta hakan da ci gaban demukuradiyya.
Tuni dai gwamnatin kasar ta bakin kakakinta Ange-Maxime Kazagui, ta yi na'am da zabin majalisar tare da fatan ba anyi hakan ne ba don haifar da wani rudani a cikin majalisar ba.
Kamar yadda kundin tsarin majalisar ya tanada, za'a zabi wani sabon shugaba cikin kwanaki uku masu zuwa.