Moroko: Fiye Da "Yan Ci-Rani 300 Suka Tsira Daga Halaka
(last modified Sun, 28 Oct 2018 09:16:10 GMT )
Oct 28, 2018 09:16 UTC
  • Moroko: Fiye Da

Sojan ruwan Moroko ne su ka sanar da ceto mutane 308 da mafi yawancinsu sun fito ne daga Afirka

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato cewa Mutane 187 daga cikin wadanda aka ceto din sun fito ne daga kasashe arewa da sahara da kuma ita kanta kasar ta Moroko.

Rahoton ya ci gaba da cewa; Mutane suna cikin kwale-kwale ne guda 16 masu tafiya da iska, sai dai sun sami matsala a cikin tekun medtreniya da kuma tekun Atlantica,abin da ya sa sojojin na Moroko kai musu dauki da ceto da su.

A kowace shekara dubban 'yan gudun hijira ne suke bi ta kasar Moroko domin kutsawa cikin kasashen turai.

Wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya ya ambaci cewa daga farkon wannan shekara ta 2018 da ake ciki zuwa yanzu, mutane 43,000 suka isa kasar Spain, dubu 38 daga cikinsu sun bi ta hanyar ruwa ne