Wasu 'Yan Bindiga Dadi Sun Kashe Wani Dan Jarida A Kasar Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33821-wasu_'yan_bindiga_dadi_sun_kashe_wani_dan_jarida_a_kasar_somaliya
Wasu gungun 'yan ta'adda sun aiwatar da kisan gilla kan wani dan jarida a gefen birnin Mogadishu fadar mulkin kasar Somaliya.
(last modified 2019-01-16T07:30:45+00:00 )
Oct 28, 2018 19:22 UTC
  • Wasu 'Yan Bindiga Dadi Sun Kashe Wani Dan Jarida A Kasar Somaliya

Wasu gungun 'yan ta'adda sun aiwatar da kisan gilla kan wani dan jarida a gefen birnin Mogadishu fadar mulkin kasar Somaliya.

Majiyar rundunar 'yan sandan birnin Mogadishu fadar mulkin kasar Somaliya a yau Lahadi ta sanar da cewa: Wasu gungun 'yan ta'adda sun kai hari kan wani dan jarida mai suna Abdullahi Muhammad Hashi da ke aiki a wani gidan radiyo, inda suka kashe shi a yankin Eelasha Biyaha da ke gefen birnin Mogadishu fadar mulkin kasar.

Abdullahi Muhammad Hashi yana aiki ne da gidan radiyon Darus-Sunnah, kuma matashi ne da ya shahara a fagen aikin jarida a wannan yankin.

Rundunar 'yan sandan birnin na Mogadishu suna ci gaba da gudanar da bincike da nufin gano mutanen da suke da hannu a kisan nashi musamman ganin babu wata kungiya da ta dauki alhakin kisar.