Gwamnatin Kaduna Ta Sassauta Dokar Ta Bacin Da Aka Sa A Jihar
Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Nijeriya ta sanar da sassauta dokar ta bacin da ta sanya a garin Kaduna, babban birnin jihar da kewaye biyo bayan rikicin da ya barke a jihar da yayi sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyi.
A wata sanarwa da gwamnatin jihar Kadunan ta fitar dauke da sanya hannun, Samuel Aruwan, kakakin gwamnan jihar Kadunan Malam Nasiru El-Rufai ta ce an sassauta dokar ta bacin ta hana zirga-zirgar da aka kafa, ta yadda a halin yanzu al'ummar garin na Kaduna da kewaye za su iya fita don gudanar da ayyukansu tun daga karfe 6 na safe zuwa karfe 5 na yamma.
Sanarwar ta kara da cewa, dokar ta bacin hana zirga-zirga din za ta ci gaba da aiki daga karfe 5 na yamma zuwa 6 na safe har sai illa masha Allah, tana mai kiran al'ummar jihar da su ci gaba da gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da girmama doka, bugu da kari kan sanya ido kan duk wani abin da zai iya haifar da rikici a jihar.
Gwamnatin jihar Kadunan dai ta dau wannan mataki ne bayan wani taro da majalisar tsaro ta jihar ta gudanar a jiya Lahadi karkashin jagorancin gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai inda ta ce bayan dubi cikin yanayin da ake ciki ta kuduri aniyar sassauta dokar ta bacin wacce a kwanakin baya aka kafa ta hana zirga-zirga na tsawon sa'oi 24 don magance rikicin da ya kunno kai a garin na Kaduna da kewaye biyo bayan kisan gillan da aka yi wa wani sarkin gargajiya a jihar.