Sojojin Najeriya Sun Ci Gaba Da Kashe 'Yan Shi'a
Sojojin gwamnatin Najeriya sun bude wuta akan mabiya mazhbar Shi'a da ke tattakin arba'in a kusa da birnin tarayya Abuja
Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ambato cewa daruruwan 'yan shi'ar kasar sun gudananr da Zanga-zanga suna masu yin kira da a saki jagoransu na harka Islamiyya, sheikh Ibrahim Yakubu El-zakzaky.
A jiya an ambaci cewa adadin wadanda su ka kwanta dama sanadiyyar kisan da sojojin su ka yi musu a yankin Cujo ya kai 16,yayin da wasu masu yawa su ka jikkata.
Tun a ranar 13 ga watan Disamba na 2015 ne aka kame Shekih el-zakzaky tare da mai dakinsa malama Zinat, bayan kisan gillar da aka yi wa daruruwan mabiyansa a birnin Zaria.
A shekaran jiya Lahadi ma an sami wadanda su ka kwanta dama sanadiyyar bude musu wuta da sojoji su ka yi a yankin Zuba.