Mo Ibrahim Ya Damu Game Da Rikici A Afirka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33848-mo_ibrahim_ya_damu_game_da_rikici_a_afirka
Shahararen atajirin nan na Sudan, Mo Ibrahim, ya nuna matukar damuwarsa kan dalilan da ke janyo rikice-rikice da kafuwar kungiyoyi masu dauke da makamai a Afrika.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Oct 30, 2018 12:02 UTC
  • Mo Ibrahim Ya Damu Game Da Rikici A Afirka

Shahararen atajirin nan na Sudan, Mo Ibrahim, ya nuna matukar damuwarsa kan dalilan da ke janyo rikice-rikice da kafuwar kungiyoyi masu dauke da makamai a Afrika.

A rahoton da gidauniyar ta Mo Ibrahim ta fitar kamar yadda ta saba a ko wacce shekara, kan iya tafiyar da mulki a Afrika, shugabanta ya bukaci shugabannin Afrika dasu maida hankali wajen rage haihuwa, da kuma samar da ayyukan yi ga matasa, wanda shi ne ummul aba'isin kafuwar kungiyoyi masu dauke da makamai irinsu Boko Haram da Al'shabab a nahiyar.

Rahoton gidaauniyar na shekara ta 2018, ya ambato cewa ana samun ci gaba sannu a hankali a nahiyar, kuma kasashen dake kan gaba su ne Maurice, Seychelles da Cap-Vert, musammen wajen iya tafiyar da mulki na gari.

Haka zalika a cewar rahoton akwai kasashen da suka bada misali mai kyau irinsu Kenya, Morocco, da Ivory Coast wacce ita ce ta samu matsayi mai kyau wajen iya jagoranci.

Kasashen da rahoton ya ambato a matsayin na karshe su ne Libiya, Sudan ta Kudu da kuma Somaliya.