Dole A Daina Kashe-Kashe A Najeriya_Buhari A Kaduna
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33852-dole_a_daina_kashe_kashe_a_najeriya_buhari_a_kaduna
Shugaba Mahammadu Buhari na Najeriya ya ce dole kashe-kashe na rashin hankali da ake a kasarsa musamman a jihar Kaduna a dainasu.
(last modified 2018-10-30T19:00:53+00:00 )
Oct 30, 2018 19:00 UTC
  • Dole A Daina Kashe-Kashe A Najeriya_Buhari A Kaduna

Shugaba Mahammadu Buhari na Najeriya ya ce dole kashe-kashe na rashin hankali da ake a kasarsa musamman a jihar Kaduna a dainasu.

Buhari ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kai a Kaduna yau Talala, tare da bayyana matukar rashin jin dadinsa game da rikicin da aka yi a jihar.

Shugaban na Najeriya ya gana da sarakuna da malaman addinai da kuma shugabanninn al'umar da rikicin jihar ya shafa.

A yayin ziyarar shugaba Buhari ya umarci jami’an tsaro da su tabbatar sun kama duk masu hannu a wannan lamari na kisan mutane ba gaira ba dalili, domin gurfanar dasu gaban shara’a.

A baya bayan nan dai jihar ta Kaduna na fama da rikicin kabilanci da na addini, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama da jikkatar wasu, lamarin da ya kai ga sanya dokar hana zirga zirga a jihar da kewaye.